Syria: Tattaunawar Kungiyar Kurdawa Da Gwamnatin Damascuss Ba Ta Yi Armashi Ba

Kungiyar Kurdawan Syria “Syrian Democratic forces” ta sanar da cewa jagororinta sun gana da jami’an gwamnatin Damascuss, inda su ka tattauna hanyoyin da za a

Kungiyar Kurdawan Syria “Syrian Democratic forces” ta sanar da cewa jagororinta sun gana da jami’an gwamnatin Damascuss, inda su ka tattauna hanyoyin da za a shigar da mayakansu cikin rundunar sojan kasar Syria.

Bayanin ya ci gaba da cewa, daga cikin wadanda su ka je Damascuss din da akwa shugaban kungiyar Mazlum Abdi, Suz Dar Haji, da Hassan Ali, da kuma wasu jagororin kungiyar.

Wani jami’in kungiyar ta “Syrian Democratic Forces” ya fada wa kamfanin dillancin labarun  Faransa cewa, kungiyar tasu ta mika wa mahukuntan Syria rubutaccen bayani akan yadda za a hade mayakansu da sojojin kasar Syria. Kurdawan suna son ganin an raba mayakan nasu a karkashin runudunoni uku, daga ciki da akwai runduna ta musamman ta mata da za kai su yankunan da suke da iko a ciki, kuma ya zamana su ne za su kasance kwamandojinta.

Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai ministan harkokin wajen Syria As’ad Shaibani ya bayyana cewa, sun karbi jawabi daga kuniyar akan tasu shawarar da su ka gabatar akan batun shigar da mayakan a karkashin ma’aikatar tsaro.

Ana ci gaba da samun sabanin a tsakanin bangarorin dangane da batun na shigar da mayakan Kurdawa a karkashin sojojin gwamnati Syria, da a wani lokaci yake kai wa ga yin fada.

Ita mai dai wannan tattaunawar ta jiya Lahadi ba ta kai ga cimma wani sakamako ba akan kawo karshen batun hadewar sojojin biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted