Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da Amurka kan keta dokokin kasa da kasa a Venezuela.
Firaministan Spain ya ce abun tir ne ” karya dokokin duniya a Venezuela.
Finland ta yi kira da a mutunta dokokin kasa da kasa bayan matakin Amurka a Venezuela.
Shugaban kasar Finland Alexander Stubb ya ce dole ne dukkan kasashe su mutunta dokokin kasa da kasa bayan matakin soja da Amurka ta dauka a Venezuela inda ta kama Shugaba Nicolas Maduro.
Koriya ta Arewa a nata bangaren ita ma ta yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai wa Venezuela wanda ta danganta a matsayin “mafi girman nau’in keta hurumin Venezuela.
Pyongyang ta yi gargadin cewa halin da ake ciki a Venezuela na iya haifar da “mummunan sakamako” ga dangantakar kasa da kasa.
Malaysia ma ta ce aikin Amurka a kan Venezuela ‘keta dokokin kasa da kasa.
Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ya yi kira da a saki Shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa nan take.
Anwar ya yi gargadin cewa “tubewa da karfi” na shugaban da ke kan mulki yana lalata tsarin kasashen duniya, yana mai jaddada cewa dole ne mutanen Venezuela su yanke shawara kan makomar Venezuela ta hanyar tattaunawa.
Slovakia ma ta soki matakin da Amurka ta dauka a Venezuela.