Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai wa Venezuela da kuma kame Shugaba Nicolás Maduro, tana mai bayyana shi a matsayin “kai hari kan ikon mallakar kasa mai ‘yanci.”
“Wannan harin yana wakiltar ci gaba da manufofin Amurka marasa adalci da tsoma baki, wanda burinsu na mulkin mallaka ya haifar,” in ji kungiyar a cikin wata sanarwa.
Hamas ta kara da cewa irin wadannan manufofin Amurka “sun jefa kasashe da dama cikin rudani, kuma suna barazana kai tsaye ga zaman lafiya da tsaro na duniya.”
Kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya, Majalisar Dinkin Duniya da cibiyoyinta, musamman kwamitin Tsaro, da su dau mataki.
Ita ma kungiyar Jihad Islamic ta soki harin na Amurka kan Venezuela.
Kungiyar ta kuma ce hare-haren sojojin Amurka sun bayyana ainahin manufar mamaye, Da kuma keta dokokin kasa da kasa da kuma ikon mallakar kasa, kuma ya nuna wata dabarar mulkin mallaka ta mamaye kasashe da kuma kwace dukiyarsu.
Kungiyar ta lura cewa Venezuela ta fuskanci hari saboda matsayinta na kasa da kasa na kullum, musamman goyon bayanta na dogon lokaci ga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu da masu adawa da ita a yankin Yammacin Asiya, da kuma goyon bayanta ga Falasdinawa da ke fuskantar kisan kare dangi da laifukan yaki.
Ta kara da cewa yakin da kasar Venezuela ke yi na ‘yanci ba zai rabu da gwagwarmayar da al’ummomin da aka zalunta ke yi kan mulkin mallaka na zamani ba.
Kungiyar ta nuna cikakken goyon baya ga Venezuela, mutanenta da gwamnatinta ta halal wacce Shugaba Maduro ke jagoranta.