Kasashen Liberia Da DRC Sun Zama Sabbin Mambobin Kwamitin Tsaron MDD

Kwamitin tsaro na MDD ya yi maraba da sabbin mambobin da ba su da hakkin hawa kujerar naki, da su ka hada Bahrain, Columbia, DRC,

Kwamitin tsaro na MDD ya yi maraba da sabbin mambobin da ba su da hakkin hawa kujerar naki, da su ka hada Bahrain, Columbia, DRC, Lativa da kuma Liberia.

Kasashen biyar da suka shiga kwamitin za su zauna ne har na tsawon shekaru biyu kafin a sake zabar wasu.

Kasar DRC ta shiga cikin kwamitin ne a karon farko a cikin shekaru 35.

Mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar ta DRC, Noƫlla Ayeganagato Nakwipone ta ce kasarsa za ta mayar da hankali wajen shimfida zaman lafiya a duniya. Haka nan kuma ya ce:

“Za mu bayar da gudun mawarmu ga MDD a ayyukan zaman lafiya.”

Haka nan ta kara da cewa; Kasantuwar kasar wacce ta karbi bakuncin rundunar shimfida zaman lafiya na tsawon fiye da shekaru 20, ta sami kwarewa wajen fuskantar kalubalen da ake fuskanta da kuma rauni da cibiyoyin suke da shi.

Ita kuwa kasar Liberia ta shiga cikin kwamitin tsaron ne a karon farko tun 1961.

Jakadan kasar a MDD Lewis Garseedah Brown II ya bayyana cewa: Kasar Liberia ta shiga cikin kwamitin tsaron ne dai cikin kwarewar da take da ita, da kuma zummar aiki da dokokin kasa da kasa.”

Haka nan kuma ya ce; sun shiga cikin kwamitin ne domin kafa hanyoyin bunkasa alaka da kasashe, da kuma aiki cikin hadin kai domin ganin an gina duniya mai cike da zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted