Trump: Mu Za Mu Mulki Venezuela Har Zuwa Lokacin Zabe

Shugaban kasar Amurka Donald Trump wanda ya gabatar da taron manema labaru a jiya ya bayyana cewa Amurka za ta Mulki kasar ta Venezula har

Shugaban kasar Amurka Donald Trump wanda ya gabatar da taron manema labaru a jiya ya bayyana cewa Amurka za ta Mulki kasar ta Venezula har zuwa lokacin yin zabe.

Shugaba Donald Trump wanda ya gabatar da taron hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen kasar, ya bayyana cewa; abinda zai biyo bayan kama shugaban kasar Venezuea Nicolas Maduro da maidakinsa, shi ne; Kasarsa za ta shiga adama da ita a cikin harkokin man fetur din kasar ta Venezuela, don haka za su sake gina cibiyar man fetur da kuma zuba hannun jari a ciki.

Shugaban kasar ta Amurka ya kuma kira yi masu ci gaba da goyon bayan shugaba Maduro da su sauya sheka ko kuma su yi mummunan karshe kamar yadda ya bayyana.

Har ila yau shugaban kasar ta Amurka ya ce, za su jira su gani ko idan mataimakiyar shugaban kasar ta Venezuela Maria coria za ta iya tafiyar da sha’anin mulkin kasar. Dama ya bayyana cewa ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya tattauna da ita, ta wayar tarho.

Da aka yi masa tambaya akan kasar China wacce take da hannun jari mai yawa a kasar venzuezuela, shugaban kasar ta Amurka ya ce, yana da kyakkyawar alaka da China, don haka za ta rika samun man fetur daga kasar ta Venezuela ba tare da wata matsala ba.

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted