Kungiyar ta agaji ta kasa da kasa ta ce, matakin da Isra’ila take dauka na janye rijistar kungiyar, wani bugun mummuke ne mai hatsari a fagen aikin ceto,wanda kuma ba zai zama karbabbe ba.
Bugu da kari, kungiyar ta ti gargadin cewa; yadda Isra’ilan ta janye rijistar bayar da dama ga gomman kungiyoyin ceto,wani tsari ne da ta yi cikin ganganci, saboda hana su gudanar da ayyukansu na agaji a cikin Gaza da kuma yammacin Kogin Jordan.
Dama dai a makon da ya gabata ne Haramtacciyar Isra’ilan ta fitar da wata sanarwa da ta bai wa kungiyoyin agaji masu yawa sa’o’i 36 da su dakatar da ayyukan da suke yi a cikin Gaza da yammacin Kogin Jordan.
“Yan Sahayoniyar sun riya cewa ba su mika bayanan ma’aikatansu ba na cikin Gaza da kuma wadanda su ka zo daga waje.
Daga cikin kungiyoyin da akwai “Action Aids” da “Doctors Without Borders” da kuma wasu da dama.
Wannan matakin na ‘yan sahayoniyar ya sa wasu kasashen turai 9 da kuma Karin kasar Japan su ka fitar da jawabin hadin gwiwa na kada karaurawar hatsari akan ayyukan agaji a Gaza.Kasahsen kuwa sun hada, Birtaniya, Canada, Denmark, Finland, Faransa da Swedeen. Sai kuma Iceland, Japan, Norway da Swiss land.
Ma’aikatun harkokin wajen wadannan kasashen sun fitar da sanarwa ce ta bai daya akan damuwarsu saboda wannan matakin na “Isra’ila da zai kara jefa Falasdinawan cikin tabarbarewar yanayi.
Kasashen sun bayyana matakin da cewa; wani bababba bala’i ne.” Haka nan kuma sun ce, farafen hula a cikin Gaza suna cikin mawuyacin hali mai tayar da hankali, ga shi kuma ana karatar lokacin sanyi. Kuma da akwai mutane miliyan 1.3 da suke da bukatuwa da taimako na matsungunni.