Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Syria “ Mirsad” ta fitar da rahoto akan yadda jami’an tsaron kasar su ka kai hare-hare a yankin gabar Ruwan kasar,tare da kama mabiyan mazhabar “Alawiyya” da yawa a cikin kwanaki biyu na bayana nan.
Garuruwan da aka kai hare-haren sun hada da Homah ta yamma, da Homs, a kokarin rufe bakin al’ummar yankin da suke nuna kin amincewa da take musu hakkoki da ake yi.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Mirsad” ta bayyana cewa; Jami’an tsaron sun kai hare-hare masu hatsari akan mata da malaman addini, da ya hada da kame Sheikh Ahmad Habib wanda fitaccen malami ne.
Haka nan kuma an kama shugaban mazhabar Alawiyya a garin Tartus, Sheikh Ali Halhal. A garin Lazikiyya an kama mata da dama da suke a cikin fagen siyasar.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Syria ta ce, Manufar wannan abinda jami’an tsaron suke yi shi ne jefa tsoro a cikin mutanen kauyuka da biranen da aka kai wa harin,musamman ma dai a cikin kauyukan Fadyu da Damasrakhu.
Mazauna wadannan kauyukan sun fuskanci barazana daga mahukunta akan za a gurfanar da su a gaban shari’a idan har su ka watsa bayanai akan abinda aka yi musu.
A wani labarin daga kasar Syria, sojojin HKI sun yi kutse cikin yankin Dar’ah da marecen jiya Juma’a.
Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa, sojojin mamayar sun yi kutse cikin yankin a kusa da tafkin “Yarmuk”, sai dai daga baya sun janye.