Akalla Mutane 15 Ne Su Ka Kwanta Dama A Wani Hari A Gabashin DRC

Kungiyar da take kiran kanta: Kawancen Kungiyoyin Demokradiyya” mai alaka da “ISIS” ta kai hare-hare a wasu kauyuka 3 dake gabashin kasar ta DRC, da

Kungiyar da take kiran kanta: Kawancen Kungiyoyin Demokradiyya” mai alaka da “ISIS” ta kai hare-hare a wasu kauyuka 3 dake gabashin kasar ta DRC, da haka ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane.

Majiyar soja a yankin na gabashin DRC ta sanar da cewa; A shekaran jiya da dare ne, kungiyar ta kai hare-haren a cikin kauyukan Katanga, Mayindilo da Kilonj dake yankin Lobiro a gundumar Kivo.

Majiyar ta ce, an rika jin harbe-harbe tun daga karfe 8;00 zuwa 10;00 na dare da hakan ya jefa mazauna yankunan cikin razana, tare da cewa; adadin wadanda su ka kwanta dama sun kai 15, yayin da gidajen 13 su ka kone.

Mai Magana da yawun soja a yankin, Mark Ilongo ya fada wa wata kafar watsa labaru ta Faransa cewa; sojojin kasar da kuma abokan kawancensu na Uganda suna bin sawun abokan gabar da su ka jefa mutanen yankin cikin razana da tsoro a lokacin da suke bikin shiga sabuwar shekara.

Ita dai kungiyar ta “Kawancen Kungiyoyin Demokradiyya” an kafa ta ne a cikin 1990’s, kuma ta kashe dubban fararen hula a cikin gabashin kasar ta DRC. Haka nan kuma ta shahara da wawashe dukiyar mutanen karkara da yi musu kisan gilla.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted