Shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya ce; a cikin sabuwar yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Gwamnatin yankin Somaliland da Isra’ila Somaliland ta amince da sake tsugunar da Falasdinawa tare da karbar bakuncin sansanin soji na “Isra’ila” domin samun amincewar kasashen duniya.
A cikin jawaban kafafen yada labarai, Mohamud ya bayyana amincewar Tel Aviv da Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta ba zato ba tsammani abu ne da ba za a taba amincewa da shi ba, kuma na nufin Isra’ila itace ta farko tun 1991 da ta amince da yankin a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Ya ce gwamnatin tarayyar Somaliya na ci gaba da kokarin sake hadewa cikin lumana, inda ya kara da cewa, Somaliland ta amince ta shiga cikin yarjejeniyoyin daidaita al’amura da Isra’ila da aka sanya wa hannu a shekarar 2020 tsakanin “Isra’ila,” da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain, da Sudan, da Maroko don daidaita dangantakarsu.
Mohamud ya zargi “Isra’ila” da neman iko a kan hanyoyin ruwa masu mahimmanci, ciki har da Bahar Maliya, Tekun Fasha, da Tekun Aden, yana mai cewa amincewa da Somaliland ya yi daidai da wani shiri na sirri a baya.
Ya jaddada cewa “Isra’ila” ba ta yin aikin “domin zaman lafiya” a maimakon haka tana neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa Somalia.