Jaridun “Isra’ila”: Da Akwai Yiyuwar Barkewar Yaki A Tsakanin “Isra’ila” Da Hizbllah

Jaridar “Isra’el Home” ta buga labarin dake cewa, bayan gushewar wa’adin kwance damarar yakin Hizbullah a kasar Lebanon, jami’an tsaron Isra’ila suna jiran shawarar da

Jaridar “Isra’el Home” ta buga labarin dake cewa, bayan gushewar wa’adin kwance damarar yakin Hizbullah a kasar Lebanon, jami’an tsaron Isra’ila suna jiran shawarar da Netantahu zai yanke, domin fada yaki.

Rahoton ya kuma ce, a cikin watannin bayan rundunonin tsaron Haramtaccitar kasar Isra’ila suna cikin shiri domin yaki da Hizbullah da suke hasashen cewa zai dauki kwanaki kadan ne,abinda kawai suke jira shi ne umarni na siyasa.

Haka nan kuma rahoton ya ci gaba da cewa, abinda sojojin suke son yi, shi ne kai hare-hare a cikin kudancin Lebanon har zuwa cikin birnin Beirut.

Jiragen yakin Haramtacciyar kasar ta Isra’ila suna cikin makaman da za ayi amfani da su,kamar yadda rahoton ya ambata domin kai hare-hare a wasu yankuna da fararen hula masu yawa suke ciki.

Haramtacciyar kasar ta yahudawa tana cewa, a shirye take ta hana kungiyar Hizbullah sake gina sojojinta.

A gefe daya,kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta sha bayyana cewa,ba za ta ajiye makamanta ba, sai dai a tattauna hanyar da sake tsara salon amfani da su a karkashin dabarun tsaro na kasar Lebanon.

Babban magatakardar kunngiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya fada a baya cewa; kasa, makami da ruhi a hade suke wuri daya, babu yadda za a raba ba. Haka nan kuma ya furta cewa;koda sama da kasa za su hade babu yadda za a yi kungiyar ta ajiye makamanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted