Rahotanni daga yankin Darfur na kasar sudan sun ambaci cewa an kashe kwamandan rudnunar kai daukin gaggawa ” RSF” a yankin Darfur, a garin Zanjali.
A wata sanarwar da rundunar ta “RSF” ta fitar ta bayyana cewa sojojin Sudan ne su ka yi wa Hamid Ali Abubakar isan gilla ta hanyar hari da jirgin sama maras matuki.
Shi dai Hamid Ali Abubakar ya kasance kwamandan rundunar ” Zararren Takobi” dake karkashin “RSF” dake da hannu a hare-haren da aka kai a yankin na Darfur.
An kama samarin garin Zanjali da dama bisa zarginsu da cewa suna yi wa sojojin Sudan leken asiri da ya kai ga sanin inda Abubakar yake da kuma yi masa kisan gilla.
Kasar Sudan dai ta fada cikin yakin basasa tun a tsakiyar watan Aprilu na 2023 a tsakanin sojojin gwamnati da kuma rdunar “RSF”. Ya zuwa yanzu dai dubban mutane ne su ka rasa rayukansu, yayin da wani adadi na mutane da ya kai miliyan 13 su ka yi hijira.
Ana zargin dakarun kai daukin gaggawa da aikata laifukan yaki a duk inda su ka kwace iko.
Gwamnatin kasar sudan tana zargin UAE da taimakawa kungiyar ta kai daukin gaggawa da makamai da kudade. Kasar ta kai karar mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa kotun manyan laifukan duniya bisa wannan zargin da take yi ma ta. Sai dai kotun ta yi watsi da karar bayan da ta ce babu kwararan dalilai akan hakan.