An gudanar da bukukuwan shigowar sabuwar shekara a kasashen duniya daban daban daga ciki har da kasar China wacce take daga cikin kasashen duniya wadanda shekarar take fara shigowa ta wajensu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an yi wasan wuta da kuma kide-kide da raye-raye da wakoki da dama a biranen kasar China da dama a dai dai shigowar sabuwar shekara ta 2026.
A birnin Beijing babban birnin kasar China an yi irgen karshe na ficewa shekarar da ta gabata wato 2025 a wani bangaren na Katanga mai tarihi na kasar wato Juyongguan. An kuma kada kararrawan Yonggle mai tsufan shekaru 600.
A birnin Wuhan na lardin Hubei an yi wasan wuta kan dogayen gine-gine na birnin wadanda suka haskaka birnin da fitillu masu launuka daban daban. Sannan a birnin Jilin nab akin ruwan kogin Songhua an yi amfani da kayakin wasan haske har 60,000 don haskaka samaniyar birnin a lokacin shigowar sabuwar shekarar.
A kasar Falasdinu da aka mamaye kuma, kakakin kungiyar Hamas a Gaza ya taya kiristoci Falasdinawa murnan shigowar sabuwar shekara ta 2026 ya kuma gabatar da jajensa ga kissan kiyashen da suke fuskanta a hannun HKI hatta bayan an yi abinda ake kira tsagaita budewa juna wuta.
Hazem Qassem ya taya falasdinawa kiristoci murnar shigowar sabuwar shekarar miladiyya ta 2026. Da fatan shekarar zata kawowa Falasdinawa al-khairi mai yawa.
Amma a dayan bangaren kuma HKI ta yi maraba da sabuwar shekarar miladiyya tare da cilla makaman igwa da kuma hare-hare kan falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nusairat da ke arewacin zirin gaza, kamar yadda ta saba a shekarar da ta gabata. Hakama ta kai hare-hare da jiragen yaki a garin Rafah na kudancin gaza a daren na sabuwar shekara.