A kasar Siriya kuma jami’in tsaro guda ne ya rasa ransa a wani coci a birnin Halan na arewacin kasar, sannan wasu abokan aikinsa biyu suka ji rauni, a lokacinda suka tsaida wani dan ta’adda suna kuma bincikensa, sai ya tada damarar boma boman da ya nade a jikinsa.
Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya makalto ministan harkokin cikin gida na kasar Siriya, Nour Al-Din Al-Baba yana fadawa tashar talabijan ta Al-Akhbariya na kasar kan cewa da alamun wanda ya yi kokarin kai hari a wani coci a birnin Halab a daren sabuwar shekara, dan kungiyar Daesh ne, saboda sune suke da irin wannan halin na kashe kowa.
Ya ce Allah ya takaita abin kan wani jami’in tsaro guda, kuma da ya sami damar shiga cocin Allah dai ya san irin barnan da zai yi.
Harin daren shigowar sabuwar shekara a birnin Halab ya auke ne a unguwar Bubal Faraj na birnin kuma babu wata kungiya ko wani mutum wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin. Sai dai ana zaton yan kungiyar Daesh ne suka shirya harin, a dai-dai lokacinda ake ci gaba da bincike don gano wanda ya kai harin, daga inda ya fito da kuma sanin wani abu dangane da shi.
Shugaban kasar Siriya dai tsohun dan kungiyar Daesh ne wanda Amurka ya zuba kudade a matsayin lada da duk wanda ya kama shi, amma daga karshe ta kama shi, sannan ta sake shi ya jagoranci kifar da gwamnatin shugaba Asad kimani shekara guda Kenan.