A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da yanzu haka ke gudana a Morocco, Najeriya ta lallasa Uganda 3-1, yayin da Tunisia da tanzania suka tashi canjaras 1-1 a wasansu na jiya Talata.
Haka zalika a jiyan DRC ta lallasa Botswana da 3-0 sai kuma Senegal da da ta yi kaca-kaca da Benin da ci 3-0.
A yau Laraba idan an jima akwai karawa tsakanin Equatorial Guinea da Aljeriya, Haka kuma akwai fafatawa tsakanin Sudan da Burkina Faso.
Akwai kuma karawa tsakanin Gabon da Ivory Coast.
A yayin da Mozanbique zata fafatawa da Kamaru.
Tuni dai kasashen da suka hada da Mali, Morocco, Afrika ta Kudu, Masar da kuma Najeriya da Aljeriya da Senegal da Tanzania, Benin da DRC suka tsallake zuwa rukunin ‘yan 16 da za’a fara bugawa a ranar Asabar kafin sakamakon wasannin cike gurbin na ‘yan 16 a yau Laraba.