Iran Da China Zasu Hada Kasashen Biyu Da Layin Dogo Ta Kasar Afghanistan

Shugaban hukumar Jiragen kasa na kasar Iran Jabbar Ali Zakiri ya tattaunawa da mataimakin ministan ayyukan raya kasa na kasar Afghanistan Abdulkaren Fateh dangane da

Shugaban hukumar Jiragen kasa na kasar Iran Jabbar Ali Zakiri ya tattaunawa da mataimakin ministan ayyukan raya kasa na kasar Afghanistan Abdulkaren Fateh dangane da shinfida layin dogo wanda zai hada kasar Iran da China amma ta kasar Afghanisatan a wannan karon.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya na cewa gwamnatin kasar Iran tana son hada garin Herat da kuma Balkh na kasar Afganistan da layin dogo, wanda kuma zai hada Iran da kasar Turkiyya, sannan zuwa kasashen Turai ta kasar Afghganistan da asiya ta tsakiya sannan zuwa kasar China.

Labarin ya kara da cewa idan shirin ya tafi kamar yadda aka tsara yawan harkokin kasuwanci tsakanin Iran da Afganistan zuwa ton miliyon 1.5 a shekara mai zuwa. Kuma zai ci gaba da karuwa.

Labarin ya kammala da cewa, idan layin dogo tsakanin Herat da Balkh ya kammala zai hada kasar Iran da kasashen Asiya da Turai, kuma zai maida kasar Afganistan a matsayin kasa ta wucewar kayaki mai muhimmanci a yankin.

Labarin ya ce an gudanar da taron ne tsakanin jami’an gwamnatocin kasashen biyu ne a birnin Kabul babban birnin kasar Afganisatan

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted