Fiye da bakin haure 3,000 ne suka mutu a teku a kokarin isa Spain a 2025

Fiye da bakin haure 3,000 ne suka mutu a teku a kokarin isa Spain a shekarar 2025. Wani rahoto da kungiyar kare hakkin ‘yan cirani

Fiye da bakin haure 3,000 ne suka mutu a teku a kokarin isa Spain a shekarar 2025.

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin ‘yan cirani ta Spain ta fitar ya nuna cewa bakin haure 3,000 ne suka rasa rayukansu a teku a kokarin isa kasar Spain a shekarar 2025 mai shirin karewa.

A cewar kungiyar, yawancin mace-macen da aka samu har zuwa ranar 15 ga Disamba sun faru ne a kan hanyar Atlantika tsakanin Afirka da Tsibirin Canary, wanda aka dauka a matsayin daya daga cikin mafi hadari a duniya.

Rahoton na Caminando Fronteras, bisa ga shaidar iyalan ‘yan cirani da kuma kididdiga na hukuma kan mutanen da aka ceto, ya tabbatar da sabbin alkaluma daga Ma’aikatar Cikin Gida ta Spain.

Kusan rabin shiga kasar ba bisa ka’ida ba ta faru ne ta hanyar kaura ta Atlantika, daga gabar tekun Yammacin Afirka zuwa Tsibirin Canary.

Daga cikin wadanda abin ya shafa da Caminando Fronteras ta rubuta akwai yara 437 da mata 192.

Kungiyar ta kuma lura da karuwar adadin jiragen ruwa da ke barin Afirka, wadanda galibi ke kan hanyarsu ta zuwa Tsibirin Balearic na Ibiza da Formentera a cikin Tekun Bahar Rum, Hanya mafi shahara wajen kwararar bakin haure daga Somaliya, Sudan, da Sudan ta Kudu a shekarar 2025, a cewar kungiyar.

Adadin mace-macen da ke kan wannan hanyar ya ninka sau biyu a wannan shekarar, inda ya kai 1,037, idan aka kwatanta da shekarar 2024, a cewar kungiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted