Iran Ta Karrama Yan Wasan Da Suka Ki Yarda Su Kara Da Yan Wasan Isra’ila

A lokacin gudanar da bikin a jiya litinin a birnin Tehran , dan wasan da yaki yarda ya kara da dan wasan Isra’ila tun a

A lokacin gudanar da bikin a jiya litinin a birnin Tehran , dan wasan da yaki yarda ya kara da dan wasan Isra’ila tun a shekarar da ta gabata an karrama shi  da kyautar girmamawa ta kasa, saboda nuna goyon bayansu da suka yi ga alummar falasdinu da ake zalunta

Bikin ya tattaro manyan yan  wasa daga bangarori daban-daban da suka hada da iyalain shahida da manyan jami’an hukumar wasanni da haka yake kara tabbatar da matsayin iran na nuna goyon bayansu ga alummar falasdinu da ake zalunta .

Kin amincewa da yan wasan suka yi su fafata da wakilan gwamnati isra’ila ya nuna adawa da manufofin isra’ila ga alummar falasdinu, kuma yana nuna jajircewar iran wajen adawa da zalunci da mamayar isra’I’la, Bikin da aka yi da yammacin jiya litinin ya samu halartar sayyed mohammad shervani mataimakin ministan wasanni da matasa na kasa tare da wasu manyan jami’ai a hukumar wasanni ta kasa da kuma tsoffin yan wasa, kuma an karrama yan wasa guda 20 daga bangarori daban daban a wajen bikin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted