An Kaddamar Da Zaben Shugaban Kasar Afirka Ta Tsakiya Ba Tare Da Tangarda Ba

Masu sa ido akan zaben kasar Afirka Ta Tsakiya suna nuni da cewa zaben shugaban kasa da aka yi a jiya Lahadi 28/12/2025 bai sami

Masu sa ido akan zaben kasar Afirka Ta Tsakiya suna nuni da cewa zaben shugaban kasa da aka yi a jiya Lahadi 28/12/2025 bai sami tangarda ko wata gardama ba.

Wata mai sa ido akan zaben na Afirka Ta Tsakiya,  Jeanne Aurelie Ngo Balnoun ta bayyana cewa; Za mu iya fadin cewa, zaben ya tafi dadiai, domin babu kawo tsaiko na azo a gani.”

Haka nan kuma ta ce; Wakilan dukkanin jam’iyyu sun halarta, su kuma ‘yan takara sun yi abinda ya dace.”

Zaben na jiya dai an yi ne bayan da aka yi wa tsarin mulkin kasar kwaskwarima tare da cire  yawan wa’adin da dan takarar shugaban kasa zai iya tsayawa. Shugaba mai ci a yanzu Faustin Archange Touadera ne yake son a sake zabar shi a karo na uku a karkashin sabon tsarin mulkin.

Sai dai masu sukar matakin shugaban kasar sun ce, sauyin da aka yi wa tsarin mulkin yana raunana tsarin demokradiyya a kasar.

Shugaban kasar ta Afirka Ta Tsakiya yana da goyon bayan kasar Rasha wacce take da jami’an tsaro a cikin kasar da suke aikin tabbatar da tsaro. Ana kuma ganin cewa shi ne wanda zai lashe zaben da aka yi a jiya.

Adadin wadanda su ka kara kuri’ar a jiya sun kai miliyan 2.3 a zaben na shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisun dokoki, da kananan hukumomi.

Ana sa ran samun sakamakon zaben ne dai a farkon watan Janairu mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted