Iran ta jaddada bukatar kare hurimin kasar Yemen 

Iran ta sake jadadda bukatar kare hurimin kasar Yemen da kuma samun tattaunawa ta tsakanin ‘yan kasar da makomarsu. Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi

Iran ta sake jadadda bukatar kare hurimin kasar Yemen da kuma samun tattaunawa ta tsakanin ‘yan kasar da makomarsu.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan a daidai lokacin da ake samun karuwar tashin hankali a kudancin kasar ta Yemen.

Ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawa daban-daban da takwarorinsa na Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, Faisal bin Farhan Al Saud da Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan.

A yayin tattaunawarsa da ministan harkokin wajen Saudiyya, Araghchi ya jaddada bukatar aiwatar da taswirar siyasa wadda ta kunshi tsagaita wuta da kuma tattaunawa mai zurfi a cikin watanni masu zuwa.

Tashin hankali a Yemen ya kara ta’azzara a ranar 3 ga Disamba, lokacin da sojojin Majalisar Wucin Gadi ta Kudu (STC), wadanda ke samun goyon bayan Hadaddiyar Daular Larabawa, suka kwace iko da Gwamnatin Hadramawt bayan arangama da kungiyoyin da Saudiyya ke marawa baya.

A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Saudiyya ya jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun kuma tattauna dangantakar kasashen biyu da kuma wasu batutuwa na kasa da kasa.

A daya bangaren lokacin tattaunawarsa da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi kira ga dukkan kasashen yankin da su yi aiki don kiyaye hadin kai da hurumin kasar Yemen.

A nasa bangaren, ministan Hadaddiyar Daular Larabawa ya jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yemen da kuma a duk fadin yankin, yayin da ya bayyana kokarin da kasarsa ke yi na rage radadin rikicin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted