JMI ta cilla taurarin ‘yan’adam guda uku a lokaci guda tare da amfani da kumbon kasar Rasha mai suna Yoyuz a dazo da misalin karfe 4.48 na yamma agogon Tehran. Jami’an gwamnatin kasar Iran sun bayyana cewa sun cilla wadan nan taurari 3 ne a ciyar cilla taurarin ‘yan’adam na kasar Rasha mai suna Vostochny Cosmodrome, wanda kuma shi ne karo na 7 ke nan tana amfani da cibiyar don cilla taurarin ‘yan’adam.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa taurarin ‘yan adam guda ukun sun hada da Zafar 2, Paya da kuma Kauthar. Dukkaninsu kirar cikin gida 100%. Kuma ayyukansu sun hada da daukan hotunan duniya wadanda za’a iya amfani da su a fannoni daban-daban.
Labarin ya kara da cewa kafin a cilla taurarin Jakadan kasar Iran a Rasha, Kazem Jalali ya bayyana cewa cilla wadan nan taurarin yan’adam na da muhimmanci sosai a shirin sararin samaniya na kasar Iran.
A cikin jerin rubuce-rubuce da yayi a shafinsa na X Jalali ya bayyana cewa an gina taurarin yan adam guda ukun gaba daya a cikin gida, tare da aikin hadin guiwa na gwamnati da malaman Jami’o’ii da kuma wasu kamfanoni masu zaman kansu. Yace banda wannan aikin cillasu zuwa sararin samaniya ne suka hada kai da gwamnatin kasar Rasha.
Jakada Jalali ya ce taurarin yan’adam guda biyu na gwamnati ne a yayinda daya kuma na wani kamfanin gina taurarin yan adama mai zaman kansa ne a kasar.
Har’ila yau ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kafin a cilla taurarin guda ukku, ya ce shirin na zaman lafiya ne ba na aikin soje ba.