Iran Da Qatar Suna Goyon Bayan Mutanen Yemen A Rikici Kudancin kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Qatar kuma firay ministan kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani sun

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  da tokwaransa na kasar Qatar kuma firay ministan kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani sun bukaci kasashen UAE da kuma Saudiyya sun mutunta ‘yancin kasar Yemen da hadin kan kasar a rikicin da kasashen biyu suke yi a kudancin Yemen.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministocin harkokin waje na kasashen biyu suna cewa, sun tattauna ta wayar tarho dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya ta Kudu, musamman kuma a kasar Yemen, inda a cikin yan makonnin da suka gabata sojojin gwamnatin rikon kwarya na kudancin Yemen (STC) suka shiga yake da wasu mayaka masu samun goyon bayan kasar Saudia a lardin Mehrah na kudancin kasar ta Yemen.

Dangane da wannan rikicin a ranar Jumma’an da ta gabata jiragen yakin kasar Saudiya sun kai hare-hare kan sojojin STC na gwamnatin wucin gadi na kudancin kasar. Kuma tana kara horasda mutanen yankin don karfafa mayakan da take goyon baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted