Isra’ila, Amurka, da Turai na yaki da Iran_Pezeshkian

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya bayyana cewa a halin yanzu Isra’ila, Amurka dama Kasashen Turai na yaki da Iran. Mista Pezeshkian ya bayyana hakan

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya bayyana cewa a halin yanzu Isra’ila, Amurka dama Kasashen Turai na yaki da Iran.

Mista Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata hira da a wata hira ta musamman da kafar yanar gizo ta ofishin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci.

Ya ce yayin da Amurka, Turai, da Isra’ila ke yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kasar ta ci gaba a karfi fiye da kowane lokaci, a fannin soja da albarkatun dan adam, kamar yadda ya bayyana a hirar.

Shugaba Pezeshkian ya gargadi Isra’ila da Amurka game da duk wani karin farmakin soja, yana mai cewa: “Idan suka zabi su fuskance mu, za su fuskanci martani mai karfi.”

Mista Pezeshkian ya sake nanata cewa Iran a halin yanzu tana cikin “yaki gaba daya” da Amurka, Isra’ila, da Turai, yana mai tabbatar da cewa ba sa son kasarmu ta tsaya.

Wannan yakin ya fi ” muni, ya fi rikitarwa, kuma ya fi wahala” fiye da kalafafen yakin Iraki a karkashin gwamnatin Saddam Hussein a shekarun 1980.

Shugaban Iran ya jaddada cewa Amurka da Isra’ila suna matsa wa Iran lamba tare da haifar da matsalolin tattalin arziki, al’adu, siyasa, da tsaro ga kasar.

Wannan yana nuni ne da yadda Amurka ta shiga yakin da gwamnatin Isra’ila ta kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci a watan Yunin 2025 kuma ta kai hari kan wurare uku na nukiliya, wanda hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa, da Yarjejeniyar Hana Yaduwar Makaman Nukiliya (NPT), da kuma Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted