Kwamitin Tsaro na MDD zai yi zaman gaggawa game da amincewar Isra’ila da Somaliland

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kira wani zaman gaggawa a ranar Litinin, biyo bayan da Isra’ila ta amince da yankin Somaliland a matsayin

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kira wani zaman gaggawa a ranar Litinin, biyo bayan da Isra’ila ta amince da yankin Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Kwamitin Tsaron zai yi zaman ne bayan da Isra’ila ta amince da Somaliland, jamhuriya mai ikirarin cin gashin kanta wadda ta balle daga Somaliya.

A cikin wata sanarwa da Qatar da Jordan suka fitar a yammacin ranar Asabar, kasashe 21 musamman na Larabawa sun yi gargadin “mummunan sakamako” game da shawarar Isra’ila ga “zaman lafiya da tsaro a yankin Afirka” da yankin Red sea.

Gwamnatin Somaliya ta bayyana wannan mataki a matsayin “keta hakki da gangan ga ‘yancin kai” da kuma “mummunan keta dokokin kasa da kasa.”

Wannan shawarar Isra’ila ta zo ne kwanaki kadan kafin Somaliya ta karbi shugabancin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na wannan karo.

Sanarwar da Isra’ila ta bayar na amincewa da Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta ta haifar da martani daga kasashe da dama a Turai, Afirka, da Gabas ta Tsakiya.

Ƙungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta (OIC), da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) sun kuma yi Allah wadai da matakin, suna mai kiransa da keta hakkin mallaka na Somaliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted