Wani binciken da kungiyar YouGov ta gudanar ya nuna cewa kashi 63% na Amurkawa basu gamsu da tsarin tafitar da tattalin arziki na shugaban kasar Donald Trump ba.
Ra’ayin Amurkawa game da yadda Shugaba Donald Trump ke tafiyar da tattalin arziki ya tabarbare a wannan shekarar, bisa ga sabon binciken YouGov da aka gudanar wa tashar CBS News.
Kashi 37% na Amurkawa da aka yi wa tambayoyi ne kawai suka ce sun amince da tsarin tafiyar da tattalin arzikin gwamnatin Trump, idan aka kwatanta da kashi 40% a farkon watan Oktoba da kuma kashi 51% a farkon Maris.
Kimanin kashi 63% na wadanda aka yi wa tambayoyi sun ce ba su amince da tsarin tafiyar da tattalin arzikinsa ba.
Wannan binciken ya kuma nuna cewa kashi 80% na Amurkawa suna ganin samun damar kiwon lafiya yana da wahala, kashi 72% sun bayyana abinci a matsayin mai tsada, kuma kashi 77% sun ce haka lamarin yake game da gidaje.
Wannan ya zo duk da kokarin gwamnatin Trump na shawo kan Amurkawa cewa manufofinsa suna taimakawa wajen rage farashin gidaje.