Guinea : Ana Zaben shugaban kasa mai manufar maida kasar bisa tsarin mulki

Yau Lahadi al’ummar Guinea ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar mai manufar mayar da kasar bisa tsarin mulki shekaru hudu tun bayan da sojoji

Yau Lahadi al’ummar Guinea ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar mai manufar mayar da kasar bisa tsarin mulki shekaru hudu tun bayan da sojoji suka kifar da mulkin Alpha Conde.

Kimanin ‘yan kasar miliyan 6.7 da suka cacanci zabe ke kada kuri’a a zagaye na farko na zaben shugaban kasar.  

‘Yan takara takwas ne ke kalubalantar shugaban rikon kwaryar soji na kasar, Mamadi Doumbouya, ciki har da Abdoulaye Yéro Baldé da Faya Millimouno.

Haka kuma akwai tsohuwar jami’ar diflomasiyya kuma Ministar Harkokin Waje Makalé Camara, ‘yar takara mace daya tilo, da Mohamed Nabé na Alliance for Update and Progress.

Fitatun ‘yan siyasa a kasar ta Guinea kamar Alpha Condé, Cellou Dalein Diallo, da Sidya Touré, waɗanda dukkansu suna gudun hijira basa takara a zaben, inda Jam’iyyunsu suka kira magoya bayansu da su zauna a gida.

Sauran ‘yan takarar a wannan zaɓen su ne Bouna Keita, Abdoulaye Kourouma, Mohamed Chérif Tounkara, da Ibrahima Abé Sylla.

wakilai da dama daga kungiyoyin kasa da kasa kamar Tarayyar Afirka, ECOWAS, da Tarayyar Turai na sa ido a zaben .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted