Putin ya yi barazanar warware rikicin Ukraine da karfin soja_Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi barazanar warware rikicin Ukraine da karfin soja muddin Kyiv ta ki karbar hanyar lumana. Idan Kyiv ba ta son

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi barazanar warware rikicin Ukraine da karfin soja muddin Kyiv ta ki karbar hanyar lumana.

Idan Kyiv ba ta son warware rikicin cikin lumana ba, Rasha za ta warware shi da karfi inji Putin.

Ya sake nanata cewa Moscow za ta cimma dukkan manufofin aikin soja na musamman, ko dai ta hanyar diflomasiyya ko ta hanyar amfani da makamai.

A yayin zaman da ya mayar da hankali kan halin da ake ciki a fannin aikin soja na musamman, Vladimir Putin ya jaddada rashin himmar Kyiv ga zaman lafiya, a cewar shafin labarai na Russia Today.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Ukraine ke tattaunawa da kawayenta musamman na turai game da shirin zaman lafiya  na tsakanin Rasha da Ukraine da Amurka ta gabatar.

Kafin nan dai, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya tafi Florida, inda ya gana da shugaban Amurka Donald Trump don tattaunawa kan daftarin yarjejeniyar da Amurka ta gabatar wacce ta kunshi shawarwari 20 na zaman lafiya.

Shugaban Ukraine ya nuna kyakkyawan fata, yana mai cewa kusan kashi 90% na yarjejeniyar yanzu za ta samu karbuwa ga Kyiv.

Duk da haka, ya yi gargadin cewa, duk da ci gaban diflomasiyya, Rasha ba ta nuna da gaske take zuwa ga zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted