Tawagar kwallon kafa ta Najeriya da ke buga gasar kofin kasashen nahiyar Afirika yanzu haka a kasar Morocco ta samu nasarar kai wa matakin zagayen ‘yan 16 bayan ta doke kasar Tunisia a wasa na biyu da ta buga a rukunin C na gasar.
Nijeriya ta zama kasa ta biyu bayan Masar da ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin zagayen 16 a gasar. Super Eagles ta hada maki 6 da kwallaye biyu a wasanni biyu da ta buga, yayin da aka jefa mata kwallaye uku a wasa biyu.
Victor Osimhen ne ya fara jefa kwallo a ragar Tunisia tun kafin zuwa hutun rabin lokaci, bayan an dawo ne kyaftin din Nijeriya Wilfried Ndidi ya jefa ƙwallon ta biyu a minti na 51 kafin Ademola Lookman ya jefa a minti na 67.
Wasan na jiya ya kasance mai matukar armashi ganin cewa dukkanin kasashen biyu ba kanwar lasa ba ne a fagen taka leda a Afirika.