Kasashen Thailand Da Cambodia Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki

Bayan kwanaki 3 na tattaunawa, kasashen Cambodia da Thailand sun rattaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a yau Asabar. A wani bayani na hadin

Bayan kwanaki 3 na tattaunawa, kasashen Cambodia da Thailand sun rattaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a yau Asabar.

A wani bayani na hadin gwiwa a tsakanin Cambodia da Thailand wanda ma’aikatar tsaron kasar Cambodia ta watsa, ta ce a yau Asabar da rana ne za a fara aiki da tsagaita wutar yakin, kuma a karkashin yarjejeniyar fararen hula dake kan iyakar da aka yi yakin za su koma gidajensu.

Har ila yau wani sashe na yarjejeniyar  afa, za a bar sojoji a inda suke a yanzu ba tare da wani sauyi ba, ko kara yawansu saboda kaucewa sake dawowar rikici.

Ministocin tsaron kasashen Thailand  da na Cambodia su ka rattaba hannu akan yarjejeniyar tsaron da ta kawo karshen kwanaki 20 na yaki a tsakaninsu.

Mutane da dama ne  su ka rasa rayukansu yayin da wasu masu yawa su ka jikkata. Haka nan kuma wasu kusan rabin miliyan ne su ka yi hijira daga yankunan da ake fada a kan iyaka.

Kasashen biyu dai suna da sabani akan iyakar dake tsakaninsu mai tsawon kilo mita 817 da ya samo asali tun lokacin mulkin Faransa akasar Cambodia. Fadin bayan nan wanda  afara a cikin watan Yuli, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 32 a dukkanin bangarorin biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted