A yau Asabar sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar ta yahudawa su ka killace garuruwa 10 a yammacin Kogin Jordan tare kuma da kai hare-hare a garin Qubadhiyya dake Jenin.
Sojojin mamayar na ‘yan sahayoniyar sun fake da batun harin da wasu Falasdinawa ‘yan gwgawarmaya su ka kai a shingen “Shahmona’yi” domin takurawa mutanen yammacin kogin Jordan.
Harin na sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila dai yana zuwa ne adaidai lokacin da ‘yan share wuri zauna suke kai hari a garin Ramallah da nan ne cibiyar mulkin gwamnati kwarya-kwarya ta Falasdinu da shugabanta Mahmud Abbas Abu Mazin yake tafiyar da Mulki.
Majiyar tashar talabijin din ‘almayadeen’ daga kasar Lebanon ta ce; “Yan share wurin zauna din sun kai hari akan motocin Falasdinawa a bakin garin Bal’in.
A cikin garin Qhubadiyya kuwa sojojin mamayar suna amfani da motocin buldoza wajen rusa gidajen mutane da mayar da su sansanonin soja, bayan da su ka killace garin ta kowace kusurwa.
Haka nan kuma wata motar buldoza din ta karce titin “Jabaluz-Zakarinah” dake cikin wannan gari. A jiya Juma’a ne dai sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka sanar fara kai farmaki a cikin garin na Qubadhiyya dake arewacin yammacin Kogin Jordan bisa cewa, wanda ya kai hari a Bisan, ya fito ne daga wannan garin. ‘Yan sahayoniya 6 ne su ka jikkata sanadiyyar wancan harin