Kungiyar masu dauke da makamai ta Saraya Ansar al-Sunna ta yi ikirarin kai harin ta’addanci a masallacin Homs.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a Telegram, Ta bayyana cewa dakarunta sun “fashe wasu na’urori masu fashewa” a cikin masallacin.
Dama wannan kungiyar ta dau alhakin kai hari kan wani coci a Damascus a watan Yuni.
Akalla mutane takwas ne suka mutu a ranar Juma’a a wani fashewa da aka yi a Masallacin Imam Ali Bin Abi Talib, wani wurin ibada na al’ummar Alawite a Homs, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Syria SANA ya ruwaito.
Wani jami’in Ma’aikatar Lafiya ta Syria ya ce akalla mutane 18 sun jikkata, ya kara da cewa wadannan alkaluma na farko ne kuma za su iya karuwa.
Issam Naameh, wani jami’in yankin, ya ce fashewar ta faru ne a lokacin sallar Juma’a, wanda galibi shine lokacin da masallatai suka fi cunkoso.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Syria ta bayyana harin a matsayin “yunkurin wargaza kasar, tana mai shan alwashin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.