A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da yanzu haka ke gudana a Morocco, Angola ta yi kunnen doki 1-1, da Zimbabwe, yayin da Masar ta lallasa Afrika ta Kudu da 1-0 a wasansu na ranar Juma’a.
Haka zalika a jiyan Zambia da Comoros sun tashi kunnen doki 0-0 sai kuma Morocco mai masaukin baki da ita ma ta yi kunnen doki 1-1 da Mali.
A yau Asabar idan an jima akwai karawa tsakanin Benin da Bostwana, Haka kuma akwai fafatawa tsakanin Senegal da DRC, kafin daga bisani Uganda da Tanzania su kece raini, sai kuma Najeriya da Tunisia.