Babban kwamandan sojojin ruwa na kasar Iran Rear Admiral Shahram Irani ya bada sanarwan cewa JMI zata dauki bakwancin rawar daji na sojojin ruwa a lokaci guda a shekara ta 2026 mai kamawa, tare da halartar kasashen duniya masu yawa fiye da na baya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban kwamandar yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa JMI ta halarci ruwan daji na sojojin ruwa da dama a yankin da kuma a fagen kasa da kasa, tare da manufar karfafa rundunar sojojin ruwan kasar da kuma kyautata dankon zumunci da kasashe wadanda basa tare da kasashen yamma a duniya.
Irani ya bayyana haka ne a yau Jumma’a a wani taron bangaren bincike na sojojin ruwan kasar wanda aka gudanar a garin Nowshahr a lardin Mazandaran dake bakin ruwan Tekun Caspian a arewacin kasar Iran. Ya kuma kara da cewa a shekarar Iraniyawa ta 1402 (2025) sojojin ruwa na kasar Iran sun halarci rawar dajin sojojin ruwa na kasa da kasa har kimani 12, inda suka baje kolin karfin sojojin ruwan kasar. Haka ma tana shirin halattar rawar daji da wasu kasashen kungiyoyin raya tattalin arziki da take cikinsu, kamar kungiyar BRICS nan gaba.
Ya ce a halin yanzu runduna ta 103 ta sojojin ruwa na kasar Iran suna kan hanyar halattar wata rawar dajin da za’a gudanar a farkon shekara ta 2026 mai kamawa. Sannan zata halarci wasu guda biyu wadanda za’a gudanar a wasu kasashe makota da kuma manya-manyan tekuna a yankin.