Kungiyar RSF Ta Sake Kwace Iko Da Yankuna 2 A Arewacin Darfur Na Kasar Sudan

Mayakan RSF a Sudan sun yi ikirarin kwace karin yankuna 2 a arewacin Darfur da ke yankin kudancin kasar, a wani yanayi da mayakan ke

Mayakan RSF a Sudan sun yi ikirarin kwace karin yankuna 2 a arewacin Darfur da ke yankin kudancin kasar, a wani yanayi da mayakan ke ci gaba da kai hare-hare da kuma kisan  fararen hula mafi yawanci mata da kananan yara.

Wasu majiyoyi sun ce anga kwararar mayakan na RSF haye a mashina zuwa birnin Abu Qamra mai tazarar kilomita 200 daga arewa maso yammacin Al Fasher, yankin da Sojin Sudan da taimakon dakarun kwance ke iko da shi.

Rahotanni sun bayyana cewa tun kafin wannan mamaya, mayakan na RSF sun kai hari garin Ambro da ke da tazarar kilomita 300 da birnin na Al Fasher da ya kai ga kisan fararen hula.

Sanarwar da rundunar dakarun kai faukin gaggawar ta RSF ta fitar a yau Alhamis ta ce mayakanta sun karbe iko da dukkanin yankunan.

Cikin jihohin Sudan 18 yanzu haka RSF na iko da jihohi 5 da ke yankin Darfur a yammacin kasar, in banda arewacin yankin na Darfur ta arewa da har yanzu ke karkashin ikon Soji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted