Fitattace mai rajin kare hakkin dan Adam din nan kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya Omyele Sowore yay tir da hari da jiragen sama da kasar Amurka ta kai najeriya a yau juma’a, kuma ya bayyana lamari a matsayin keta alfarmar kasar da kuma nuna raunin shugabancin a kasar.
Yayi wannan bayani ne a cikin shafinsa na X kuma ya zargi dukkan gwamnatin najeriya da kuma Amurka kan kai harin a ranakun bikin kirsimeti a wani kauye a birnin Sokoto, da ya ce wai sun kai harin kan yan ta’adda ne a wajen.
Duk da cewa gwamnatin najeriya ta sanar cewa tana sane da kai harin, kuma ta bayyana farmakin a matsayin na hadin guiwa ne da abokan hulda na kasashen duniya, sai dai a fili yake cewa an kai harin ne ba tare da cikakken izini gwamnatin ba ko kuma wasu dake boye karkashin gwamnatin Bola Tinububa,
Daga karshe ya nuna damuwarsa game da karfin najeriya wajen kare kasarta, kuma yayi gargadin cewa ana mayar da kasar a matsayin yar kallo a muhimman batutuwan tsaro da suka shafi yan kasarta