Islami: Matsalar Washington Ita Ce Ci Gaban Kasashe Ba Makaman Nukiliya Ba

Shugaban Hukumar  Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami, ya bayyana cewa “babbar matsalar da ke tattare da gwamnatocin Amurka a jere ita ce ci gaban

Shugaban Hukumar  Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami, ya bayyana cewa “babbar matsalar da ke tattare da gwamnatocin Amurka a jere ita ce ci gaban ƙasashe, ba makaman nukiliya ba.”

Da yake jawabi a taron farko na ƙwararrun likitoci, radiotherapy, da oncology a Iran, ya ƙara da cewa, yin amfani da ƙarfi ba bisa ka’ida ko doka ba, sun ba Amurka damar cin karenta babu babbaka domin cimma muradunta ta hanyar yin fatali da dokokin ƙasa da ƙasa.”

Ya ci gaba da cewa, “Dangane da Dabaru na Tsaron Ƙasa na Amurka, manyan manufofin ci gaba sune fasahar wucin gadi, fasahar nukiliya, wani abu da ya kamata ya kasance mai sauƙin isa ga dukkan ƙasashe.”

Amma a cwwarsa a bin ban takaici Amurka ta siyasantar da komai tare da Sanya ma’ani ya zama maslaharta da muradunta kawai, ba tare da la’akari da maslaha da muradu da kuma hakkoki na sauran al’ummomin duniya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted