Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya aike da sakon taya murna ga kiristocin duniya a dalilin bikin Kirsmeti da mabiya addinin kirista ke bikin zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu.
Mista Pezeshkian ya aike da sakon murnar bikin tare da na Sabuwar Shekara ga shugaban Cocin Katolika Paparoma Leo XIV.
A a sakon da ya aike, Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa haihuwar Yesu Almasihu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) alama ce ta kyawawan halaye na ruhaniya, gami da ‘yanci, yaki da zalunci, da tausayi, wanda aka yaba a cikin Alqur’ani Mai Tsarki, littafin Musulmai.
Ya kara da cewa, ta hanyar ayyukan da suka dace yana yiwuwa a samar da sabuwar hanya zuwa ga cimma zaman lafiya, tsaro, da ‘yanci ga dukkan al’ummomin da aka zalunta.
A karshe, Pezeshkian ya bayyana fatansa na farin ciki da samun wadata ga mabiyan addinin Kirista da Paparoma Leo XIV, da kuma fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk faɗin duniya.
Yau ce ranar 25 ga watan Disamba da mabiya addinin Kirista a faɗin duniya ke bukukuwan murnar haihuwar Yesu Almasihu, wanda Kiristoci suka yi amannar cewa shi ne mai ceto.
A duk lokacin wannan biki, mabiya addinin na Kirista na shagulgulan murna da suka hada da abinci da sanya sabbin sutura da musayar kyautuka da kuma sada zumunci.