A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da yanzu haka ke gudana a Morocco, Burkina Faso ta doke Equatorila Guinea 2-1, yayin da Aljeriya ta lallasa Sudan da 3-0 a wasansu na ranar Laraba.
Haka zalika a ranar ta Laraba Ivory Coast ta doke Mozambique da 1-0 Sai kuma Kamaru wacce ta doke Gabon da 1-0
Kafin hakan a ranar Talata Najeriya ta lallasa Tanzania da 2-1, sai kuma Tunisia data doke Uganda 3-1
A gobe Juma’a idan Allah ya kai akwai karawa tsakanin Angola da Zimbabwe, Haka kuma akwai fafatawa tsakanin Afrika da Kudu da Masar, kafin daga bisani Zambia da Comoros, wadanda zasu kece raini.
Sai kuma Morocco mai masaukin baki da zata fafata da Mali.