Korea Ta Arewa Ta Yi Gwajin Sabon Makami Mai Linzami Dake Cin Dogon Zango

Kafafen watsa labarun kasar Korea Ta Arewa sun bayar da labarin cewa, shugaban kasar Kim Jung Un ya halarci inda aka yi gwajin makami mai

Kafafen watsa labarun kasar Korea Ta Arewa sun bayar da labarin cewa, shugaban kasar Kim Jung Un ya halarci inda aka yi gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango da aka harba a kusa da gabar ruwan ta gabas.

Kamfanin dillancin labarun kasar ta Korea Ta Arewa ya ce, an yi gwajin ne a karkashin bitar da kasar take yi akan muhimman kamamanta da kuma sake kera wasu sabbi na zamani da za su iya yin shawagi a sararin samaniya da nisa.

Labarin ya kuma ce, makamin ya yi nasara ta yadda ya kai bara akan inda aka harba shi da nisan kilo mita 200 da hakan yake nuni da samun nasara saboda yanzu ne ake kan ganiyar kera makamin.

A gefe daya, kafafen watsa labarun kasar ta Korea Ta Arewa sun ce a halin yanzu kasar tana kan gina jirgin ruwa mai iyo a karkashin ruwa wanda zai yi aiki da makamashin Nukiliya. Jirgin ruwan yana da nauyin ton 8700, kuma zai iya harba makamai masu linzami.

A yau Alhamis ne dai kafafen watsa labaru kasar ta Korea Ta Arewa su ka nuna hotunan jirgin ruwan na Nukiliya a a wurin da aka kera shi.

Shugaban kasar ta Korea Ta Arewa ya fadi cewa, karfafa makaman kasar na Nukiliya ya zama wajibi a cikin wannan duniyar da babu alamar an kama zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted