Yansanda A HKI Sun Yi Sun Kama Masu Bukukuwan Kirsimeti A Birnin Haifa

Majiyar labarai daga birnin Haifa da aka mamaye ya nuna cewa yansanda a haramtacciyar kasar ta hana kiristoci gudanar da bukukuwan kirsimeti a unguwar Wadi-Al-Nisnas

Majiyar labarai daga birnin Haifa da aka mamaye ya nuna cewa yansanda a haramtacciyar kasar ta hana kiristoci gudanar da bukukuwan kirsimeti a unguwar Wadi-Al-Nisnas na birnin Haifa, saboda aiwatar da dokar da HKI ta kafa na takaita ayyukan sauran addinai a kasar in banda addinin yahudawa,

Kamfanin dillancinlabarai IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labarai da daman a fadar cewa yansandan yahudawan sun kama wasu kiristoci a taron na kirsimeti a birnin Haifa, daga ciki har da wani mutum sanya da rigar kirsimeti ko Santa Claus.

Labarin ya kara da cewa yansandan yahudawan a ranar Talata, sun farwa taron kirsimeti na kiristoci larabawa kiristoci a birnin Haifa da aka mamaye, inda suka hana taron suka kuma kama wasu kiristoci. Labarin ya kara da cewa HKI ta dade da fara hanawa ko kuma takaita bukukuwan da kiristoci da musulmi suke yi a kasar.

Kuma ana gudanar da bukukuwan kirsimeti a kasar Falasdinua da aka mamaye ne cikin takurawa sosai. Wanda a nan gaba idan sun samu suna iya hana gudanar da wadan nana bukukuwa gaba daya a duk fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted