Rahotanni sun bayyana cewa kwamandan hafsa hasoshin sojin kasar libiya ya Mutu bayan da jirgin sojoji dake dauke da shi ya yi hadari jim kadan bayan barinsa birnin AnKara a wata ziyarar da ya kai kasar Turkiya, kamar yada jami’an gwamnatin kasashen libiya da turkiya suka bayyana .
Fira ministan kasar libiya Abdulhamid Dbeibah ya tabbatar da rasuwar mohammad Ali Ahmad al-haddad da sauran mambobi guda 4 da suke mara masa baya, kuma ya bayyana lamarin a matsayin wani bala’I da fadawa kasar da rundunar sojin kasar .
Tawagar kasar libiya ta yi kwanaki a garin Ankara inda ta tattaunawa da ministan tsaron kasar turkiya Yasar Guler da sauran kwamandojin sojan kasar ta turkiya, ziyarar ta zo ne adaidai lokacin da ake gudanar da ayyukan hadin guiwar sojoji tsakanin turkiya da kuma kasar Libiya.