A wani bayani mai karfi da ya fitar a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya jakadan iran Amir Saeid Iravani ya bayyana cewa kuduri mai lamba 2231 da yayi Magana kan shirin nukiliyar iran tarihinsa ya kare tun a ranar 18 ga watan oktoban shekara ta 2025, don haka ba zai yi wu a dauki wani mataki karkashinsa ba, kuma yayi tir da matakin da Amurka ta dauka tare da bayyana shi a matsayin sabama doka, kuma ya yi kira dasu koma kan turbar diplomasiya mai amfani.
Wannan jayayyar tana nuna irin zaman tankiya dake kara Kamari tsakanin Iran da Amurka kan shirin ta na nukiliya da kuma makomar yarjejeniyar JCPOA, musayar ra’ayin ya kara tabbatar da zurfin dake tsakanin dokar hana yaduwar makamashin nukiliya da kuma ayyukan diflomasiya tsakanin kasashen biyu.
Jakadan iran a majalisar dinkin duniya Amir saeid iravani ya caccaki bayanan da magoya bayan Amurka suka yi, kuma ya jaddada hakkin iran na mallakar fasahar nukiliya don ayyukan zaman lafiya, yace Amurka tana matsin lamba ne kan dakatar da tace yuraniyom baki daya, lamarin da ya sabawa hakkin Iran bisa dokar NPT kuma wani mataki ne naman biyan wasu bukatun siyasa .
Wakilin Amurka ms Ortega yayi ikirarin cewa iran ba ta da hakkin tace sinadarin yuraniyom a cikin kasarta, don haka Amurka tana son tattaunawa ne kai tsaye da kasar iran .