Janar Hatami: Sojojin Iran Suna Sa Ido Akan Kai Da Komawar Makiya A Wannan Yankin

Kwamandan rudnunar sojan Iran Janar Amir Hatami ya bayyana cewa, kasar tana bin diddigin kai da komowar abokan gaba a cikin wannan yankin,kuma duk wani

Kwamandan rudnunar sojan Iran Janar Amir Hatami ya bayyana cewa, kasar tana bin diddigin kai da komowar abokan gaba a cikin wannan yankin,kuma duk wani wuce gona da iri da za su yi, zai fuskanci mayar da martani mai tsanani.

Janar Hatami ya bayyan hakan ne dai a lokacin da yake ziyartar rudnunar sojan Iran dake yammacin kasar, tare da kara da cewa, a halin yanzu sojojin Iran suna cikin Shirin ko-ta-kwana domin fuskantar kowace irin barazana.

Janar Hatami ya kuma ce, ya kai wannan ziyarar ne, domin sake yin bitar halin Shirin da sojojin suke a cikin, amma Alhamdulillahi  sojojin da suke kan iyaka suna cikin kumaji na shiri na koli. Haka nan kuma ya kara da cewa, da akwai kayan yaki na zamani bisa la’akari da abinda ya faru a lokacin yakin kwanaki 12 da Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Janar Hatami ya ce; Aikin da yake a gaban sojoji a wannan lokacin shi ne kare kasa da kuma ‘yancinta, kuma kokarin da muke yi, shi ne ganin mun aiwatar da wannan aikin cikin hanyr mafi kyawu.

Daga cikin wuraren da janar Hatami din ya ziyarta da akwai sansanin sojojin sama dake garin Kermansha da aka kai sabbin jiragen yaki a wurin

Kwanadan rundunar sojan na Iran ya yi wa sojojin da suke a wannan yankin godiya saboda kokarin da suke yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted