HKI Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Birnin Qudus

Motocin Buldoz na HKI sun rusa gidajen Falasdinawa a tsakiyar birnin Qudus a jiya Litinin, inda suka bar iyalan Falasdinawa 13 suka rasa inda zasu

Motocin Buldoz na HKI sun rusa gidajen Falasdinawa a tsakiyar birnin Qudus a jiya Litinin, inda suka bar iyalan Falasdinawa 13 suka rasa inda zasu sa kansu.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ta bayyana cewa hakan ya awku ne a unguwar  Wadi Qaddum, inda suka ci mutuncin falasdinawa mata da dama kafin su rusa gidajen.

Kafafen watsa labarin yankin sun bayyana cewa sojojin yahudawan sun tasa keyyar masu gidajen maza da mata suka fiddasu daga yankin da karfi, wanda yake kara tabbatar da kekacewar zuciyar yahudawa yan mamaya a kasar ta Palasdinu.

Labarin ya kara da cewa, yahudawan sun gabatar da dalilai na karya wanda suka hada da rashin takardun gina gidajen ko kuma gine-ginen basa bisa ka’ida kafin su rusa su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted