Tsaron Iran ba ya cikin abubuwan tattaunawa_Baghaei

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa karfin tsaron kasar bay a cikin abubuwan tattaunawa a kai. Mai magana da yawun Ministan Harkokin Wajen kasar

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa karfin tsaron kasar bay a cikin abubuwan tattaunawa a kai.

Mai magana da yawun Ministan Harkokin Wajen kasar Esmaeil Baghaei ne ya bayyana hakan.

M. Baghaei ya ce karfin tsaron Iran an tsara shi ne don dakila duk wani hari daga makiya kuma ba a shawarwari akan sa.

Lokacin da yake bayyana hakan a taron manema labarai na mako-mako a wannan Litinin, akan tambaya game da kalaman da kafofin watsa labarai na Isra’ila da Amurka suka yi game da yiwuwar kaddamar da wani sabon hari kan Iran a karkashin hujjar shirin makamai masu linzaminta.

Ya kara da cewa Iran ta samar da shirin makamai masu linzami ne don kare huruminta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted