An Kashe Wani Kwamandan Sojan Rasha A Birnin Moscow

A birnin Moscow na kasar Rasha an sanar da cewa an kashe wani babban kwamandan sojan kasar ta hanyar tashin bom a cikin motarsa a

A birnin Moscow na kasar Rasha an sanar da cewa an kashe wani babban kwamandan sojan kasar ta hanyar tashin bom a cikin motarsa a yau Litinin.

Hukumar bincike ta tarayyar Rasha ta ce, janar din da aka kashe shi ne shugaban bangaren bayar da horo na Babbar cibiyar sojan kasar.

Laftanar janar Fanil Sarvarov ya rasa ransa ne sanadiyyar fashewar wani bom da aka dasa a karkashin motar da yake tafiya a cikinta a yankin kudancin birnin Moscow.

Fashewar bom din ya kuma lalata motoci da dama da suke a kusa da inda aka kashe janar din.

Jami’an gwamnatin kasar ta Rasha sun ce, kisan gillar da aka yi wa janar din, yana da alaka da jami’an leken asirin kasar Ukiraniya, domin a baya sun yi amfani da abubuwa masu fashewa irin wannan wajen kashe wasu jami’an kasar.

A watan Disamba na shekarar da ta gabata wani bom ya kashe Lafatanar janar Igor Kirillov, wanda shi ne kwamandan makaman Nukiliya da makamai masu guba na sojojin Rasha. Binciken da Rashan ta gudanar ya nuna cewa kasar Ukiraniya ce take da hannu.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted