Burkina Faso, Mali Da Nijer Sun Kafa Runduna Ta Tsarin Yankin Sahel

A birnin Bamako na kasar Mali shugaba kasa Janar Assimi Goita ya jagoranci bikin kafa runduna ta yankin Sahel wanda ya hada kasashen uku wato

A birnin Bamako na kasar Mali shugaba kasa Janar Assimi Goita ya jagoranci bikin kafa runduna ta yankin Sahel wanda ya hada kasashen uku wato Mali Borkina Faso da kuma Nijer. Wannan dai shi ne mataki na baya bayan nan wanda kasashen uku na Sahel suka dauka don tabbatar da karfinsu a yankin, da kuma hana dukkan manya-manyan kasashen duniya da kuma na yankin barazana ga hadin kansu da kuma karfafa dankon zumunci a tsakaninsu.  A cikin watan Jenerun wannan shekara mai karewa ne ma’aikatar tsaron kasar Niger ta bada sanarwan cewa runduna mai sojoji 5000 zasu iya tabbatar da tsaron yankinsu na Sahel. Labarin ya kara da cewa Janar Daouda Traore na kasar Burkina faso ne zai jagoranci rundunar, wacce take da cibiya a birnin Niamey na kasar Nijer.

Bukin na Bamako ya sami halartar ministocin tsaro na kasashen uku mambobi a cikin kungiyar Sahel. Kasashen uku sun samar da kungiyar ‘Sahel Alliance’ bayan sun fice daga kungiyar ECOWAS ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted