Ministan Harkokin Wajen HKI Ya Bukaci Yahudawan Australia Su Dawo HKI Da Zama

Ministan harkokin waje na HKI Gideon Saar ya bukaci yahudawan kasar Autralia sun dawo HKI bayan hare-haren da aka kai masu a makon da ya

Ministan harkokin waje na HKI Gideon Saar ya bukaci yahudawan kasar Autralia sun dawo HKI bayan hare-haren da aka kai masu a makon da ya gabata a birnin Sydney cibiyar kasuwancin kasar wanda ya kaiga kashe yahudawa da dama.

Jaridar ARABNEWS ta kasar Saudia ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa yana yana kira ga yahudawan da suke kasashen yamma su dawo HKI. Saar yayi wannan kiran ne bayan hare-haren da aka kaiwa yahudawan Sydney na kasar Autralia wanda ya kai ga mutuwar mutane 15 daga cikinsu.

Ministan ya kara da cewa, yana kira ga dukkan yahudawa daga kasashen Faransa, Autralia, Canada da Belgium su dawo kasar HKI don kaucewa kiyayyar yahudawa da ke karuwa a wadan nan kasashe.

Tun bayan fara yaki da kungiyar Hamas a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 da ta gabata, kiyayyar yahudawan sahyoniyya ya karu a duniya saboda kisan kiyashin da suka aikata a gaza kan al-ummar Falasdinawa.

Inda ya zuwa yanzu sun kashe Falasdinawa akalla 70,000 a yayinda wasu 171.000 sun ji rauni. Kuma har yanzun sun killace yankin sun kuma hana kayakin bukatun yau da kullum shiga yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted