Firaministan Kasar Sudan Zai Gana Da Antonio Guterres A Birnin New York

Firaministan Sudan Kamil Idris, zai gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a birnin New York da nufin kawo karshen  rikicin kasar

Firaministan Sudan Kamil Idris, zai gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a birnin New York da nufin kawo karshen  rikicin kasar da kuma samun tallafin jin kai a kasar da yakin basasa ya jefa cikin mayuwacin hali.

Tsawon shekaru kasashen duniya na kokarin gani an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar sa kai ta RSF,wanda hakan ya ci tura.

kungiyoyi a ciki da wajen kasar na bayyana cewa yaki na kara tsananta a yankin Kordofan da ke kudancin kasar, wanda hakan ya haifar da fargabar kisan gilla irin wanda aka yi a lokacin da RSF ta kama El-Fasher a karshen watan Oktoba, inda rahotanni da dama suka ruwaito cewa an yi kisan gilla, fyade, da kuma kwace kayan agaji.

Antonio Guterres ya bayyana a farkon wannan watan cewa yana shirya tattaunawa da bangarorin biyu na kasar ta Sudan da basa ga maciji da juna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted