Amurka Ta Kwace Wani Karin Tankar Man Fetur Na Kasar Venezuela

Sojojin Amurka sun kwace wani jirgin ruwa dauke da man fetur a kusa da ruwayen kasar Venezuela, kuma wannan shi ne jirgi na biyu wanda

Sojojin Amurka sun kwace wani jirgin ruwa dauke da man fetur a kusa da ruwayen kasar Venezuela, kuma wannan shi ne jirgi na biyu wanda sojojin Amurka suka kwace a cikin makonni biyu da suka gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na Amurka ya sha alwashin sauke shugaba Nicola Madoro na kasar Venezuela bayan zargin da yake masa na cewa shi ne yake shugabancin kungiyar kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar Amurka.

Labarin ya kara da cewa a baya bayan na shugaban ya zargi kasar Venezuela mai arzikin man fetur da kwace kayakin kamfanonin hakar man Fetur na kasar Amurka tun lokacinda kasashen biyu suka babe a shekaru 1970 zuwa sama, a lokacinda yan kasa suka kwace iko da kasar Venezuela.

Labarin ya kara da cewa a ranar 10 ga watan  Decemban da muke cikin ne Amurka ta kwace tankan dakon mai na farko, sannan sojojin Amurka suka kwace tankar man na biyu a cikin makon da ya gabata, a likacinda yake dauke da tutan kasar Panama, kuma wadanda suka ganewa idanunsu sun tabbatar da cewa sun ga jirage masu saukar ungulu suna sauka kan jirgin daukan man a kusa da ruwayen kasar ta Venezuela.

Gwamnatocin Amurka da suka suce da kuma na shugaba Trunp dai sun dade suna dorawa kasar Venezuela takunkuman tattalin arziki masu tsanani don durkusar da gwamnatin kasar. Amma goyon bayan da mutanen Venezuela suka bawa gwamnatin Nicolas Madoro da kuma na wanda ya gada Hugo Chaves sun hana gwamnatin kasar Venezuela faduwa.

Masana suna ganin gwamnatin trump ta fake da wadannan zarge zarge ne kawai don ganin bayan shugaba madoro a kan kujerar shugabancin kasar Venezuela. Idan kuma sun sami nasara, zasu dora dan korensu ne wanda zai rufe bakinsa a lokacinda suke kwasar arzikin kasar zuwa Amurka.

Shugaba Madoro dai ya musanta dukkan zargin da Amurka ta ke masa, sannan yana ganin Trump yana son kauda shi kan kujerar shugabancin kasar ne kawai. Amma ba zai nika kai ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted