An bude taron koli na Hadakar kasashen Sahel, a wannan Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali.
Taron zai hada shugabannin kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso a ranakun 22 da 23 ga Disamba.
Tun da farko dai an fara da zaman “Majalisar Ministocin kungiyar wanda ya hada ministocin da ke kula da harkokin kasashen waje, tsaro, da kuma wadanda ke tsara batutuwan ci gaba.
Za su yi taro na tsawon kwanaki biyu, har zuwa Lahadi, a karkashin jagorancin Janar Assimi Goïta na Mali, shugaban kungiyar AES na yanzu.
Taron zai ba da dama don yin bitar shirye-shiryen da aka yi don karfafa tsarin kungiyar na musamman a Yammacin Afirka da kuma zabar shugabanta na gaba.
Taron karo na biyu na Kwalejin Shugabannin kasashen na hadakar Kasashen Sahel zai fayyace ci gaban da aka samu, a karƙashin shugabancin Mali, a tsawon shekara ta farko ta Ƙungiyar AES.
Sauran muhimman abubuwa sun haɗa da kammala aiwatar da Ƙungiyar AES da kuma magance batutuwan da suka shafi ƙungiyoyinta na tarayya, yanki, da na duniya.
A wannan yanayin, Shugabannin Ƙasashen za su sake duba ayyukan da aka gudanar a fannonin tsaro, diflomasiyya da ci gaba, da sadarwa.
Yaƙi da ta’addanci, daidaita ayyukan diflomasiyya, da aiwatar da matakai masu ƙarfi da nufin inganta yanayin rayuwa na al’ummar yankin AES su ne ginshikan zaman.